Liverpool ta sayi Andrew Robertson na Hull City

Kungiyar kwallon kafa ta Hull City ta sayi dan wasan bayan kulob din Hull City Andrew Robertson a kan fam miliyan takwas.

Dan wasan tawagar Scotland din ya ce yarjeniyar ta kwashe lokaci mai tsawo ana yinta kuma ya ce farashinsa zai iya karuwa zuwa fam miliyan 10.

Robertson ya ce yana farin cikin komawa Liverpool. “Babu wani kulob na musamman kamar Liverpool,” in ji shi.

Dan wasan ya koma Hull City ne a kan fam miliyan 2.85 a shekarar 2014 kuma ya yi mata wasa sau 39 a kakar bara kodayake kulob din ya fita daga Gasar Firimiya.

Har ila yau, ya ce: “Yayin da nake tasowa na yi fatan buga wasa a manyan kulob kamar Liverpool saboda haka yanzu burina ya cika.

“Ina so na nunawa mutane cewa zan iya a wasa a wannnan mataki kuma ina burin taka muhimmiyar rawa a wannan kakar,” in ji shi.

Robertson shi ne dan wasa na uku da Liverpool ta saya a kakar bana, bayan Mohamed Salah wanda ta saya daga Roma da kuma Dominic Solanke daga Chelsea.

Asalin Labari:

BBC Hausa

787total visits,1visits today


Karanta:  Neymar zai yi wa PSG wasa a yau Lahadi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.