Lokacin Sauya Fasalin Najeriya Ya Yi – IBB

Yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan batun makomar Najeriya tun bayan da takaddama tsakanin masu rajin neman kasar Biafra da kungiyar matasan arewa da suka ba kabilar Igbo wa'adin ficewa daga arewacin kasar, tsohon shugaban Najeriya a lokacin mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce lokaci ya yi da za a sauya fasalin Najeriya.

shugaban Najeriya a lokacin mulkin soja, Gen. Ibrahim Badamasi Babangida, ya bi sahun masu kiran da a sake wa Najeriya fasali, yana mai cewa lokaci ya yi da za a yi hakan.

Babangida ya yi wannan kiran ne a sakonsa da ya fitar na bikin karamar salla, wanda aka rabawa kafafen yada labarai ciki har da Sashen Hausa na Muryar Amurka.

Tsohon shugaban ya ce samar da sauyi ga fasalin kasar zai magance kalaman batancin da ake jefa wa juna musamman a wannan lokaci.

“Ina mai goyon bayan ragewa bangaren gwamnatin tarayya karfin iko, a mikawa gwamnatocin jihohi, yayin da ita kuma gwamnatin tarayya a bar ta da kula da fannin harkokin waje da tsaro da kuma tattalin arziki.” Sanarwar ta Babangida ta nuna.

Ya kara da cewa “batun ka ga hanyoyin mallakar gwamnatin tarayya a garuruwa da birane ya zama tsohon yayi yana kuma bukatar a sake dubi akan sa, hakan na nufin dole ne mu sauya tunani akan kundin tsarin mulkinmu domin mu shigar da sabbin dabaru domin karfafa kasarmu.”

Sai dai tsohon shugaban ya ce batun cewa kasar ba ta cimma burinta ba, ba dalili bane da zai sa a rusa abin da “kakanninmu suka gina shekaru da dama ba.”

“Abin da ya fi cin rai a tarihin Najeriya shi ne yakin basasan da aka yi na tsawon shekaru 30 tsakanin watan Yulin 1967 zuwa watan Janairun 1970 inda mutane da dama suka rasa rayukansu.”

Babangida ya kuma nuna bukatar a samar da ‘yan sandan jiha a maimakon dogaro da na tarayyar, inda ya ce “tsoron da ake yi a da cewa gwamnoni za su yi amfani da su wajen biyan bukatunsa, ba zai yi wu ba, domin yanzu mutane sun farga.”

Karanta:  Muna Nan Muna Kokari Don Ganin Buhari Ya Sake Tsayawa Zabe 2019 – El-Rufai

Babangida ya ce ya yi amfani da mika gaisuwar wannan sallar ne domin ya mika wannan sakon ga ‘yan Najeriya lura da cewa ana ta kai ruwa rana kan makomar kasar.

Wannan sanarwa da tsohon shugaban ya fitar na nufin shi ma ya shiga sahun sun tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar wanda ya jima ya na kira da a sake sauyin fasalin Najeriya.

Asalin Labari:

VOA Hausa

699total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.