Madrid ta Lashe Kofin gasar Spanish Super Cup

Real Madrid ta lashe kofin Spanish Super Cup na bana, bayan da ta lallasa Bercelona da ci 2-0 a wasa na biyu da suka kara da daren ranar Laraba a filin wasa na Santiago Berneabue.

Madrid, wadda ke rike da kambun gasar zakarrun Turai da ta Spania dai, ta kuma sha gaban Bercelona wajen murza leda a wasa duk da cewa babu Cristano Ronaldo a ciki.

Marco Asensio da Karim Benzama ne suka zura wa Bercelona kwallayen biyu tun kafin a je hutun rabin lokaci

A zageyen farko na wasan wanda aka yi a Nou Camp, Real ce ta doke Barcelona da ci 3-1, abinda ke nufin Real Madrid din ta doke Barca da ci 5-1 jimilla.

Kungiyoyin biyu manyan abokan hamayya ne a duniyar tamaula abinda ya sa nasarar Madrid din ta saka magoya bayan Barca suka dugunzuma.

Asalin Labari:

BBC Hausa

707total visits,1visits today


Karanta:  'Yan Sandan Spain Sun Kashe Maharin Barcelona

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.