Madrid za ta gabatar da Vallejo ga magoya baya

Real Madrid ta sanar cewar a ranar Juma’a za ta gabatar Jesus Vallejo ga magoya bayanta a Santiago Bernabeu.

Kuma wannan ne karon farko da dan kwallon mai tsaron baya mai shekara 19 zai saka rigar kungiyar ya kuma taka filin wasa.

Madrid ta sayi Vallejo daga Zaragoza a shekarar 2015, amma ta amince ya ci gaba da taka-leda a can a matsayin aro inda ya buga wasa 20.

A kakar 2016/17 Madrid ta bai wa Eintracht Frankfurt aron Vallejo, inda ya buga wasa 25 a gasar Bundesliga da aka kammala.

Vallejo dan kwallon tawagar matasa ta Spaniya shi ne ake hasashen zai maye gurbin Sergio Ramos a nan gaba kadan.

Da zarar Madrid ta gabatar da dan kwallon a gaban magoya baya, za kuma ta bai wa ‘yan jarida damar yi masa tambayoyi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1079total visits,1visits today


Karanta:  Serena Williams ta haifi 'ya mace

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.