Magajin Garin Sokoto Danbaba Ya Ajiye Rawaninsa

 

Tun a ‘yan watannin baya ne dai takaddama ta barke tsakanin  Magajin garin na Sokoto da fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na III, bisa nadin sarautar Marafan Sokoto, da mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi wa Alhaji Inuwa Abdulkadir, tsohon Ministan Wasanni da Matasa.

Kan wannan al’amari ne tsohon Magajin gari mai murabus ya nuna rashin amincewarsa da wannan nadi ta hanyar aikawa da wata wasika ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, inda yake bayyana cewa Inuwa Abdulkadir, bai cancanci wannan mukami na Marafa Sokoto ba. “Iyayen Inuwan bayi ne” a fadar Hassan Danbaba.

Asalin Labari:

VOA

731total visits,5visits today


Karanta:  Sultan Ya Tabbatar Cewa 1 Ga Watan Satumba Ita Ce Ranar Sallah

Leave a Reply

Your email address will not be published.