Mai ya sa kasuwancin gawayi Yafi kowanne kasuwancin albarka

Me Yasa kasuwancin Gawayi Yafi Kowana Kasuwancin Albarka a jihar Kano. Saboda tashin karansin da gas yasa mutane da yawa suka raja’a da girki da aiki da gawayi.

Tashin kalanzir da iskar gas ya sanya al’umma da dama sun raja’a da amfani da gawayi wajen girki.
Wannan ya sanya mutane irinsu Mallan Isa Sagiru da ke zaune a unguwar Dorayi ya koma amfani da
gawayi saboda ya taimaki kansa da kuma masu saida gawayi inda ya kara da cewar ya fi kowanne irin
nau’in girki sauki.
Mallan Isa Sagiru bayyana cewar a farkon watan Janairu da Febrairu na shakarar wannan gawayi ya
tsallake kowanne nau’in girki yadda ba a zato sakamakon farashin kalanzir da yake canzawa inda ake
sayarda kowacce lita a kan farashin N350 ko kuma abinda yah aura hakan. Gidajen mai kan sayar da
kalanzir akn farashin Naira 190 zuwa N200. “Duk da farashin kalanzir da yake sauka a hankali ni de na fi
raja’a ga gawayi” inji Nasiru Tafarki wanda ya sai lita biyu na kalanzir a wani gidan mai. Ya kara da cewa
“na sayi kalanzir din ne saboda ayi sauri a shirya yara su ta fi makaranta amma bayan wannan ba a bun
da zai sa na siya”.
Baya da tashin kalanzir, itama iskar gas ba’a barta a baya ba, inda farashin kilo biyar na iskar ta gas a kan
sayar dashi akan N1800 wanda a baya farashin sa bai wuce N1500. Farashin kilo sha biyu ya tashi daga
N3000 izuwa N4300.
Ma’aikatan ofishin kididdiga ta kasa wato (National Bureau Of Statistic) ta bada shaida kan cewar
al’umma a yankin Kano, Abuja da Jihar Oyo sun fi kowa siyan iskar gas a watan Janairu na 2017.
Mallan Shu’aibu Kabiru na daya daga cikin dilolin gawayi inda yake cewa kilo daya na gawayi suna sayar
dashi akan farashin kudi N1500 wanda suka fi samo shi daga jihar Niger ko jahohin Kogi, Kwara, Bauchi,
da Kaduna. Sai dai diloli da yawa sun fi son sayan na jihar Niger sakamakon yafi kowanne girma gami da
cikar ma’auni. Ya kara da cewa sukan kasa shi inda sukan bayar da har na N50, N100 har zuwa N800.
Mallam Kabiru Isaq ya zayyana cewa ya kwashe kimanin shekara biyar a wannan sana’a. kuma yana mai
godiya ga Allah ta yadda yak an samu riba sosai. A lokutan baya bukatar gawayi tafi karuwa a lokutan
yanayi na sanyi, amma a yanzu a kowanne lokaci akan bukaci gawayi sakamakon tsadar karanzir da iskar
gas.
Farfesa Yakubu ya bayyana cewar ya kamata gwamnati ta fadada bincike gami da rage farashin na’urorin
girki saboda asamu sassaucin rayuwa ga al’umma.

Karanta:  Kasuwar hannayen jari ta Nigeria ta yi matukar bunkasa
Asalin Labari:

Daily Trust

515total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.