Majalisa Ta Gindayawa Bangaren Zartaswa Sharudda Kafin Ta Tantance Jami’anta

Majalisar Dattawan Najeriya ta jaddada matsayinta na cewa ba za ta sake tantance sunan kowa da Fadar shugaban kasa za ta gabatar ba har sai ta cika wasu sharudda da suka hada da amincewa da cewa ita ke da hurumin tantance jami'an da za a nada a mukamai.

Majalisar wacce ta nuna rashin jin dadinta kan kin cire Ibrahim Magu duk da cewa ta taki tabbatar mai da mukaminsa, a baya-bayan nan ta ki tantance Mr Lanre Gbajabiamila da bangaren zartaswar ya mika mata.

Daga cikin sharuddan da majalisar akwai batun sai mukaddashin Shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo ya amince cewa majalisar na da cikakken hurumin tantance sunayen wadanda gwamnati za ta nada kan wasu mukamai.

A baya Farfesa Osinbajo ya furta cewa ba dole ba ne sai gwamnati ta nemi amincewar majalisa kafin ta nada mutane kan wasu mukamai a lokacin da majalisar ta sake kin tantance Ibrahim Magu.

Wadannan kalamai na mukaddashin shugaban kasar a cewar wasu masu lura da al’amura su suka harzuka majalisar.

Mukaddashin ya yi amfani da fasarar da wani babban lauya Femi Falana ya yi wa wani sashen kudurin dokar kasa kan wannan batu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

497total visits,1visits today


Karanta:  Rashin tabbatar da kujerata bai dame ni ba - Ibrahim Magu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.