Malaman Nigeria na adawa da ‘yancin kananan hukumomi

Wasu jihohi a Najeriya sun dauki tsawon watanni ba tare da biyar albashin ma’aikata ba

Kungiyar Malaman makarantar Primary ta Najeriya ta yi zanga-zanga tana neman a tsame ta daga yunkurin bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai.

Mambobin kungiyar sun yi tattaki zuwa majalisar dokoki a jihar da kuma ofishin shugaban ma’aikatan jihar domin mika kokensu.

Mukaddashin kungiyar reshen jihar, Comrade Dalhatu AbduSalam Sumaila ya ce `ya`yan kungiyar za su shiga mawuyacin hali idan suka kasance a karkashin kananan hukumomi masu cin gashin-kansu.

Hakan a cewarsu zai faru ne idan aka yi la`akari da cewa a yanzu ma da wuya ake biyansu hakkokinsu, ciki har da albashi.

Malaman dai sun bukaci a barsu a karkashin gwamnatin tarayya ko ta jiha maimakon kananan hukumomi masu cin gashin kansu.

Shugaban ma’aikata na jihar Kano, Alhaji Muhammad Auwal Na’iya ya ce gwamnati za ta yi nazarin bukatar malaman makarantar.

Batun bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai batu ne da ya dade yana janyo cece-kuce a Najeriya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

387total visits,1visits today


Karanta:  Musulmi a Kano sun gudanar da taron addu’o’i don Shugaba Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.