Man United: Jose Mourinho ya damu kan rashin sayen ‘yan wasa

Jose Mourinho ya mika harkar sayen ‘yan wasa a hannun mataimakin shugaban United Ed Woodward

Kocin Manchester United Jose Mourinho bai ji dadin rashin shirin kungiyar na sayen ‘yan wasa ba a wannan lokacin.

Bayan da United ta dauki kofin Europa a wasan karshe da ta doke Ajax ranar 24 ga watan Mayu, Mourinho ya ce ya ba wa mataimakin shugaban kungiyar Ed Woodward jerin sunayen ‘yan wasan da yake bukata.

Manyan jami’an kungiyar a asirce sun tattauna a kan sayen ‘yan wasa uku.

Watakila za a iya samun labarin sayen wani dan wasan nan gaba a makon nan, amma dai kawo yanzu dan wasa daya kawai da suka saya shi ne, dan baya Victor Lindelof mai shekara 22 daga Benfica a kan fan miliyan 31.

Ana ganin cewa Mourinho yana son akalla dan gaba guda daya domin maye gurbin Zlatan Ibrahimovic mai shekara 35, wanda ya ji rauni kuma ba zai warke ba sai sabuwar shekara, tare kuma da wani dan wasan tsakiya.

Kokarin sayen dan wasan Atletico Madrid na gaba Antoine Griezmann, mai shekara 26, a kan kudin da kila da zai kusa da wanda aka sayi dan wasan da ya fi tsada a duniya, Paul Pogba, fan miliyan 89, daga Juventus.

An dai haramta wa Atletico sayen wani dan wasa a lokacin wannan kasuwar kuma tuni Griezmann ya sabunta kwantiraginsa a kungiyar.

Haka kuma Romelu Lukaku ma da Man United din ke son saye daga Everton ya fi son ya tafi Chelsea, saboda haka Alvaro Morata, mai shekara 24 na Real Madrid shi ne ya zama babban zabinsu.

To amma shi din ma har yanzu duk wani kokari na tattaunawa a kan cinikin nasa da Real Madrid yana gamuwa da cikas.

1070total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.