‘Man Utd za ta sayarwa Madrid David de Gea’

Manchester United za ta sayar wa Real Madrid golanta David de Gea amma sai kaka mai zuwa kuma bayan kungiyar ta sayo Gianluigi Donnarumma daga AC Milan, a cewarsa jaridar Sun.

Chelsea ta bukaci Atletico Madrid ta biya fam miliyan 50 gabanin ta sallama mata Diego Costa, wanda kungiyar ta taya shi a kan fam miliyan 30, in ji jaridar Sun.

Har ila yau, jaridar Mirror ta ruwaito cewa Chelsea na neman dan wasan Inter Milan, Antonio Candreva, yayin da kungiyar ta yi masa kudi fam miliyan 25.

Liverpool ta ki sallama wa Barcelona Philippe Coutinho a kan fam miliyan 119 da kungiyar ta taya dan kwallon, kamar yadda jaridar Mirror ta bayyana.

Tottenham ta yi nisa a cinikin Juan Foyth daga kungiyar Estudiantes ta kasar Argentina a kan kusan fam miliyan 9, a cewar jaridar Guardian.

Asalin Labari:

BBC Hausa

4429total visits,1visits today


Karanta:  Man United ta yi wasa 12 a jere ba a doke ta ba

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.