Manchester Utd ta doke Real Madrid a bugun fanareti

Manchester United ta doke Real Madrid a bugun fanareti bayan sun tashi a wasan gabannin kakarsu da ci 1-1 a Santa Clara.

Anthony Martial ne ya bai wa Jesse Lingard damar fara ci wa United kwallo daga gefen hagu.

Casemiro ya daukar wa Real Madrid fansa a bugun fenareti bayan sabon mai tsaron bayan United, Victor Lindelof, ya kayar da Theo Hernandez.

A bugun fanaretin da aka yi na raba gardama bayan an tashi wasan kunnen doki, an barar da fanareti 7 daga cikin 10 inda United ta doke Real Madrid da ci 2-1.

Daren wasan bai yi wa Lindelof kyau ba, domin ya kara barar da fenareti bayan ya janyo fenaretin da ya sa Madrid ta rama kwallon da aka zira mata.

Wani labari mara dadi ga United kuma shi ne ficewar Ander Herrera wanda ya ji ciwo a kugu bayan ya buga wasan minti shida kacal.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1025total visits,2visits today


Karanta:  Ina son barin Liverpool – Philippe Coutinho

Leave a Reply

Your email address will not be published.