Matasan Arewa Sun Nufi Majalisar Dinkin Duniya Akan Biafra

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa a Karkashin jagorancin Ambasada Shettima Yarima wadanda suka ba Kabilar Igbo wa’adin watanni uku sun aikewa Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guetarres da takarda mai shafuka 20 inda suka nemi Majalisar Dinkin Duniya ta shiga batun baiwa yankin Biafra cin gashin kanta da ke neman kawo wa Najeriya matsala.

A wani taro na masamman da sukayi a Abuja, matasan sun bayyana cewa yakamata Majalisar Dinkin Duniya ta shiga maganan raba Najeriya, wanda har yanzu ya kasance barazana ga zamanta kasar daya dunkulalla.

Matasan sunyi tir da kungiyar fafutukar neman yankin Biafra. Inda suka nuna bacin ransu akan yadda shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ke ci gaba da yin tarurrukan rabewa duk da gargardin da kotu tayi masa tare da nuna halin ko in kula ga kokarin da wasu ‘yan kasa keyi wanjan dinke barakar da aka samu can baya.

Daya daga cikin jagororin kungiyar matasan arewa Sheriff Ashiru Nastura, ya ce abinda ke kunshe a cikin takarda kuka ne ga Majalisar Dinkin Duniya akan abubuwan da kungiyar IPOB, wacce Nnamdi Kanu, ke jagoranta ta keyi na kokarin raba Najeriya.

A bangaren matasan Ohaneze Ndigbo, wadanda tun can basu goyon bayan raba Najeriya suyi ikirarin cewa yunkurin ba zai haifar wa kasar da’ mai ido ba in ji shugaban matasa Ohaneze Ndigbo Maazi Okechukwu Esuguzoro.

Ya kara da cewa kabilar Igbo ta bada gagarumin gudumawa wajan gina tattalin arzikin arewa saboda haka babu inda zasu da kuma kira da babbar murya cewa a dauki matakin kyautatawa kowa harda matasan Igbo, idan aka yi haka to za a ji dadin zama tare.

Asalin Labari:

VOA Hausa

4058total visits,4visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.