Mayakan Boko Haram ‘700 sun mika wuya’

Mayakan kungiyar Boko Haram 700 ne suka mika wuya ga dakarun Najeriya, kamar yadda rundunar sojojin kasar ta yi ikirari.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya fitar ta ce mika wuyan ya biyo bayan farmakin da dakarun Najeriya suka kai ranar Litinin.

Har ila yau, Kukasheka ya ce kwarya-kwaryar binciken da aka yi ya nuna cewa akwai manyan mayakan Boko Haram a cikin mutanen da suka mika wuyan.

A ‘yan watannin nan mayakan Boko Haram sun kaddamar da munanan hare-hare, ciki har da wanda suka kai Jami’ar Maiduguri a watan jiya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

421total visits,2visits today


Karanta:  Nijeriya Bata Bukatar Tallafi Daga Kasashen Wajen Saboda Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra Wato IPOB – Gwamnatin Tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published.