Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?

Rawar da Farfesa Yemi Osinbajo yake takawa a matsayin mukaddashin shugaban kasa sakamakon rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya shafe watanni a wajen kasar na ci gaba da jan hankalin jama’a. Yayin da wasu ke cewa yana taka rawar gani, wasu kuwa cewa suke yi yana dari-dari.

Rashin lafiyar shugaban, wanda ba a bayyana takamaiman abin da ke damunsa ba, da kuma halin da kasar ke ciki ya sa fagen siyasar kasar daukar dumi a wasu lokuta.

Akwai wadanda suke ganin babu abin da ya sauya bayan da Mista Osinbajo ya fara tafiyar da kasar a watan Janairun da ya gabata.

Masu irin wannan tunanin su kan kafa hujja da yadda Farfesan ya jira sai da ya samu umarni daga Shugaba Buhari gabannin ya sanya a kasafin kudin kasar a watan Yuni.

“Akwai wasu abubuwa da za mu ce shi ne ya kirkiro su, misali akwai abubuwa da ya yi musamman ta fuskar tattalin arziki wato yadda ya yi hobbasa wajen farfado da darajar naira,” in ji Malam Kabiru Danladi Lawanti na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Ya ci gaba da cewa, “Mutum ba zai yanke hukunci gaba daya ba, tun da an ce duk wani muhimmin mataki da zai dauka sai ya tuntubi Shugaba Buhari.”

“Idan ban da tsare-tsare ta fuskar tattalin arziki, to babbu wani abu da za a ce Mista Osinbajo ya yi daban daga Buhari,” in ji Malam Kabiru.

Sai dai ana sa bangaren, Malam Mahmud Jega, mataimakin babban editan jaridar Daily Trust, ya ce mukaddashin shugaban “yana taka tsan-tsan.”

Ya ce ba ya tsammanin akwai wani mataki da ya dauka nasa na kashin kansa ba wanda Shugaba Buhari ya tsara ba.

Karanta:  Buhari ya Soke Taron Ministocin na Wannan Makon

“A duk tsawon makonnin nan da Osinbajo yake rikon-kwarya, gaskiya yana sassarawa ne ta gefe, ba ya taba manyan abubuwa na babban aikin gwamnati ko na siyasa, ko kananan abubuwa ma ba duka yake taba wa ba,” in ji Jega.

Daga nan ya ba da misalin yadda mukaddashin shugaban ya kasa nada ministoci duk da cewa Shugaba Buhari ya aike da sunayensu wadanda majalisar dattawan kasar ta amince da su, “amma a rantsar da su, a ba su mukami ya gagara”.

Game da batun tattalin arziki da ake cewa Mista Osinbajo ya tabuka wani abu yayin da Buhari yake jinya, Mahmud Jega ya ce aikinsa ne a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa.

“Mataimakin shugaban kasa shi ne shugaban da ke kula da majalisar tattalin arzikin kasa wadda ta kunshi gwamnoni da wasu manyan ministoci da kuma gwamnan babban bankin Najeriya,” in ji shi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

738total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.