Me Yasa Buhari Sahale Gina Layin Dogo Zuwa Daura

Ministan Sufuri, Mr Rotimi Amaeachi yayi Karin haske kan dalilan da yasa Gwamnatin Tarayya ta sahale gina layin dogo zuwa Daura, garin mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Jihar Katsina, inda tace yin hakan yunkuri ne na hada kasar da makwotan kasashe mussaman wanda sukayi iyaka da kasar ta yankin da bana teku ba.

Yayi bayanin cewa gwamnati ta lura cewa kasashen da sukayi makwabtaka da kasar ta yankin da bana teku ba kamar Jamhuriyar Nijar suna shigowa da kayayyakinsu ne ta Ghana, Togo dama jamhuriyar Benin saboda rashin layin dogon da zai sadar da garuruwansu.

Lokacin da yake magana da manema labarai jim kadan bayan zaman da suka sabayi duk wata kan shirin samar da layin dogo daga Legas zuwa Ibadan kan kudi $1.5bn

Amaechi yayi watsi da bayanan da wasu keyi kan sahale layin dogon inda yake cewa layin dogon ba zai tsaya a Daura kawai ba.

Yake cewa, “Mun lura cewa akwai masu gasa damu daga iyakokinmu na kasa, masu gasar damu sun hada da Ghana, Togo kai harma da jamhuriyar Benin. Saboda wadanda muke iyaka dasu ta kasa na shigowa da kayayyakinsu ta wadancan kasashen saboda bamuda layin dogon da zai kai garesu.

“Don tunkarar wannan matsalar, Shugaban Kasa ya sahale gina layin dogo wanda zai kai har ga Maradi cikin Nijar. Amma wannan layin dogon wanda zai tasu daga Kano zuwa Maradi cikin Nijar zai ratsa ta cikin wasu garuruwan. Layin dogon zai ratsa ta Kazaure zuwa Daura sannan ya wuce zuwa Jibya daga nan kuma ya karasa zuwa Maradi. Kana nufin idan layin dogon ya isa Kazaure zai bi ta iska ne ya wuce garin Daura? A a ba haka nake nufi ba, dole sai ya ratsa ta garin Daura sannan ya isa zuwa Jibya da Maradi. Abin takaici ne ace mutane na fassara cewa layin dogon za shi Daura ne kawai.

Karanta:  Gwamnatin Nigeria ce ta 35 a Afirka – Gidauniyar Mo Ibrahim

“Da wannan layin dogon ne zamu iya fuskantar gasar dake tsakaninmu da Ghana dama Togo saboda makwotanmu wadanda sukayi iyaka damu ta kasa. Kaga kenan zamu iya bugar kirji mu fadawa makwotanmu da mukayi iyaka dasu ta kasa cewa zamu iya dauko musu kayayyakinsu daga tashar jiragenmu na ruwa a Legas zuwa kasarsu.

Wani abu guda daya da nake alfahari da shi a matsayina na mutumin da keda alhakin hada dukkanin manyan biranen jihohinmu ta hanyar layin dogo shi ne, daga Daura, zamu sadar da jihar Katsina inda ya rage mana kawai saura sadarda manyan biranen jihohi guda uku, wato jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi.”

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

1204total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.