Messi, Ronaldo na cikin fitattun ‘yan wasa na duniya na 2017

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta fitar sunayen wadanda za a zabi fitaccen ‘yan kwallo na duniya daga cikin su, wadanda suka hada da Cristiano Ronaldo daga Real Madrid da Lionel Messi daga Barcelona da kuma Neymar daga Paris St-Germain.

A bara ma Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasa, bayan da ya doke Messi da Neymar da kuma Antoine Griezmann.

Kocin Chealsea Antonio Conte na iya lashe kofin gwarzon koci bayan da ya ja ragamar kungiyar har suka kai da samun nasarar lashe kofin Premier a kakarsa ta farko a Stamford Bridge.

An sake gabatar da mai rike da kofin fitacciyar ‘yar kwallo ta mata Carli Lloyd a matsayin wacce za ta lashe kofin na bana.

Lieke Martens wadda ta ci kwallo uku a wasan neman shiga gasar Euro 2017 a Netherland, da kuma ‘yar kwallon Venezuela Deyna Castellanos su ne abokan karawar Lloyd.

A ranar 23 ga watan Oktoba ne za a gabar da wadanda suka yi nasara a dakin taro na Palladium da ke Landan.

Asalin Labari:

BBC Hausa

743total visits,3visits today


Karanta:  Lionel Messi ya yi aure da rabin ransa tun suna yara

Leave a Reply

Your email address will not be published.