Morata: Dan wasa mafi tsada a tarihin kungiyar Chelsea

Chelsea ta kammala daukar dan wasan Real Madrid, Alvaro Morata kan kudi fan miliyan 60 kan yarjejeniyar shekara biyar.

Chelsea ta sayi dan wasan mai shekara 24 wanda ya ci kwallo 20 bayan da ya koma Real daga Juventus a matsayin wanda ta saya mafi tsada a tarihi.

Kungiyar mai rike da kofin Premier ta dauki ‘yan wasa hudu kenan da suka hada da mai tsaron raga Willy Caballero da mai tsaron baya Antonio Rudiger da mai wasan tsakiya Tiemoue Bakayoko.

Morata zai bi Chelsea sansanin da take yin atisayen tunkarar kakar bana a Asia.

Dan kwallon da Chelsea ta saya mafi tsada a tarihi shi ne Fernando Torres daga Liverpool a Janairun 2011 kan kudi fan miliyan 50.

Asalin Labari:

BBC Hausa

746total visits,2visits today


Karanta:  Di Maria ya yarda da laifin kin biyan haraji

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.