Mourinho da Conte sun yi cacar-baki

Cacar-baki ta barke tsakanin kocin Chelsea Antonio Conte da na Manchester United Jose Mourinho, inda Conte ya ce ya kamata ya kashe wutar gabansa ya daina sa ido a harkokin wasu.

Mourinho ya yi suka akan koci-koci da suke korafi a kan ‘yan wasansu da suke jinya, bayan da kungiyarsa ta yi nasara a karawar da suka yi da Benfica da ci 1-0.

Mourinho ya ce, “Ba na magana akan wani dan wasana da ya ji rauni, amma wasu koci-kocin kuka suke yi idan dan kwallonsu ya yi rauni, a tunanina ba yi wa ‘yan wasan kuka ne mafita ba, mayar da hankali a kan ‘yan wasan da suke da lafiya shi ya fi dacewa don su samu kwarin gwiga.

Da a ce zan yi kuka kamar yadda wasu suke yin kuka to da nayi kuka a kan Ibrahimavich, da Pogba, da Fellaini amma ban yi kuka ba saboda ba na yi”.

“Kowanne lokaci Mourinho yana sa ido da kuma yin shisshigi akan a al’amuran da suke wakana a Chelsea, ni a ganina kamata ya yi mutum ya kashe wutar gabansa, ba ya sa ido a al’amuran wasu ba,” in ji Conte.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1538total visits,1visits today


Karanta:  Man City ta sayi Benjamin Mendy na Monaco

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.