Mu Ibon Arewa Ne, Don Haka Ba Inda Za Mu — Igwe Godwin

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Sarkin Ibo mazauna Yola, fadar jihar Adamawa, Igwe Godwin Omenka, Eze Ibo 111 ya bayyana matakin da kungiyar matasan Arewacin Nijeriya ta dauka na bada wa’adi ga al’umman Ibo su bar yankin da cewa babban kuskure ne.

Da ya ke magana da manema labarai a Yola, Eze Ibo 111, ya ce masatan na arewa sun mance da cewa al’umman Ibo wani bangare ne na kasar baki daya.

“Ibo su fice daga Adamawa da jihohin arewa? Suma wani bangaren jama’ar yankin da al’adun arewa ne ba bakin haure ba. Nijeriya kasarmu ta gado ne, mu ‘ya’ ya da jikokin wannan muhimmiyar kasa mu barta mu tafi ina? Ibo ‘yan kasa ne a kowace jiha, domin su wani bangaren ci gaban jihar ne.

“Idan mun tafi kudu, mun zama baki a can, arewa ita ce gidanmu, mafiyawanmu a nan aka haifesu sun tashi a nan arewa, a nan muka yi makaranta a nan muka yi aure, muna da kyakkyawan dangantaka kuma mu haifuwar nan ne, mu Ibon arewa ne, don haka ba inda za mu,” in ji shi.

Shugaban al’umman Ibo da ke Jihar Adamawa ya kuma yi kira ga jama’ar Ibo da ke harkokin kasuwanci a yankin da cewa su ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba, ya ce “ku ci gaba da kasuwancinku kamar ba abin da ya faru, saboda a gida kuke.

“Mutanen Ibo mutane ne masu son zaman lafiya, ku ci gaba da ba da gudumuwar ci gaba duk inda ka samu kanka,” in ji Igwe

Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya dama ta jihohi da su daukin matakin kare dukiyoyi da rayuka da dukiyoyin jama’ar Ibo, ya ce bai kamata wasu su yi amfani da wannan dama wajan lalata mu su dukiyoyi ba, kana ya yi addu’ar samun zaman lafiya da dorewar kasar a matsayin abu guda.

Karanta:  An Kirkiri Kungiyar Hangen Nesa Ta Tallafawa Lafiya Wato ‘’Visionary for Sustainable Health Support Foundation’’ (VSHSF)
Asalin Labari:

LEADERSHIP Hausa

347total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.