Mummunar Guguwa Ta Juye Ambaliyar Ruwa a Texas

Sama da mutum dubu guda aka tseratar daga yankunansu bayan mahaukaciyar guguwar nan da ta afkawa jihar Texax a Amurka ta haifar da kakkarfan ruwan saman daya juye zuwa ambaliyar ruwa a Houston.

A cewar hukumar kula da yanayi ta kasar, karfi da kuma yawan ambaliyar ruwan kan ma’aunin centi mita 50 ba kakkautawa ya dakatar da zirga-zirga tare da sanya razani a zukatan mutanen yanki, lamarin daya tilasta kwashesu don kare lafiyarsu.

Haka kuma yawan ruwan saman ya sanya koguna da dama yin ambaliya a yankin abin daya kara tsananta halin da al’ummar ke ciki, inda kuma masu aikin ceto suka gaza karasawa wasu wuraren da annobar ta tsananta.

Ya zuwa yanzu dai hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum biyu ciki har da wata mata da ruwa ya janyo gangar jikinta kan titi.

Tuni dai hukumomi suka yi gargadin kauracewa zirga-zirga face wadanda suke a yankunan da basa cikin hadarin samun ambaliyar ko kuma wadanda aka kwashe zuwa wasu yankunan.

Wannan dai ita ce mafi munin guguwa a Amurka tun bayan ta Charley a watan Agustan shekarar 2004 da kuma ta Hurricane data afkawa Texas a shekarar 1961 wadda ta halaka mutum 34.

Mummunar guguwar ta haddasa katsewar wutar lantarki a mafi yawancin sassan jihar ta Texas, kuma yanzu haka kimanin jami’an agaji dubu daya da dari takwas ne ke aikin bayar da ceto

Asalin Labari:

RFI Hausa

426total visits,3visits today


Karanta:  Korea Ta Arewa na tallafa wa ta'addanci- Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.