Musulman Rohingya Dubu 60 Sun Nemi Mafaka a Bangladesh

Tuni dai Hukumar bada tallafin abinci ta duniya ta dakatar da bada tallafin abincin ga jihar ta Rakhine mai fama da rikicin.

Wasu ‘yan Rohingya da ke neman mfaka a Bangladesh

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, akalla Musulman Rohingya dubu 60 ne suka tsere zuwa Bangladesh a cikin kwanaki takwas sakamakon rikicin da ake fama da shi a jihar Rakhine da ke Myanmar.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Vivian Tan ta shaida wa kamfanin Dillancin labaran Faransa na AFP cewa, akwai yiwuwar adadin Musulman da ke neman mafaka a Bangladesh ya karu nan gaba.

Tuni dai Hukumar bada tallafin abinci ta duniya ta dakatar da bada tallafin abincin ga jihar ta Rakhine mai fama da rikicin.

Ana zargin ‘yan tawayen Rohingya da haddasa rikicin na baya-bayan nan sakamakon harin da suka kai kan jami’an tsaro a ranar 25 ga wata Agustan da ya gabata.

Rahotanni na cewa, kimanin mutane 400 da suka hada da fararen hula suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan.

Asalin Labari:

RFI Hausa

557total visits,2visits today


Karanta:  Zaben Kenya: Sakamakon farko ya nuna Kenyatta ya sha gaban Odinga

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.