Musulman Rohingya na Fuskantar Wariya – Amnesty

Kungiyar kare hakkin dan'adam ta Amnesty International ta ce musulmai 'yan Rohingya a Myanmar na fuskantar wani nau'in wariya mai kama da ta launin fata karkashin jagorancin gwamnati.

Rahoton baya-bayan nan na Amnesty ya bayyana kauyukan Rohingya a matsayin kurkukun talala, inda ya al’ummomin suka shafe gomman shekaru suna fuskantar musgunawa.

Mai aikowa BBC rahoto daga Kudu maso Gabashin Asiya na cewa rahoton Kungiyar Amnesty daya ne daga cikin takardun da kungiyoyin kare hakkin dan’adam ke tattarawa da yiwuwar shigar da manyan hafsoshin sojan Bama k’ara a Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

Amnesty ta ce gallazawa mutane ta karu matuka tun a shekara ta 2012, lokacin da tarzoma tsakanin mabiya addinin Buddha da Musulmi ta karade jihar Rakhine.

Daruruwan dubban ‘yan Rohingya ne tun daga lokacin suka tsere zuwa Bangladesh mai makwabtaka.

Sai dai, jagorar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta ce tana fatan cim ma wata yarjejeniya nan gaba kadan da Bangladesh kan yadda ‘yan Rohingya za su koma gida.

‘Yan Rohingya dubu 600 ne suka tsere daga kasar tun cikin karshen watan Agusta lokacin da sojoji suka kaddamar da wani gangamin tashin hankali a kansu.

Bayan wani taro da ministocin kasashen wajen Asiya da na Turai, Ms Suu Kyi akwai bukatar duk abin da zai yiwu don tabbatar da kwanciyar hankali a jihar e, inda rikici ke faruwa.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1086total visits,1visits today


Karanta:  Ambaliyar Ruwa Mafi Muni a Afirka a Shekara 20

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.