Mutane sama da 345 ne suka rasa rayuka a girgizar kasa a Indonesia

Indonesia earthquake
Indonesia earthquake

Hukumomi a Indonesia sun bayyana cewar mutane sama da 345 ne suka rasa rayukan su a sanadiyar girgizar kasa da ta afku a yankin skakatawa na Lombok kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Antara ya ruwaito.

Mafiya yawa sun rasa rayukan nasu ne a Kayangan dake arewacin tsuburin, kamar yadda Antara ta bayyana.

Kusan mutane 200,000 ne ke zaune a yankin na arewacin Lombok, wanda yake wani sashe mai yawan tsaunika kamar yadda kididdiga ta nuna a shekara ta 2010.

A jiya Talala hukumomi sun bayyana cewa akalla mutane 20,000 ke neman agajin gaggawa da kuma kashi 80 na ginunnuka da zuka lalace.

“Mun samu damuwa matuka ta yadda kayan agaji suka kasa shiga wannan yankin sakamakon rushewar gidaje., inji wani ma’aikacin Red Cross dake Jakarta mai suna Husni Husni.

696total visits,6visits today


Karanta:  'Yan Kunar bakin wake sun kashe mutane 12

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.