Mutum 4 sun rasa rayukansu, 8 kuma sun jikkata sakamakon fashewar bam a Maiduguri

A kalla mutum hudu sun rasa rayukansu, takwas kuma sun jikkata yayin harin kunar bakin wake ranar Talata a Maiduguri. Mutum hudun sun hada har da ‘yan kunar bakin waken.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne a Garejin Muna dake Maidugurin babban birnin jihar Borno. Inda daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken ya tada Bam din dake jikinsa, ya kasha kansa da mutum biyu da kuma jikkata mutum takwas.

Ance daya daga cikin maharani kuma yayi kokarin fisgar harsashi daga gurin wani soja kafin wani Jami’in ya harbe shi har lahira

“Na farkon dai ya tada bam din dake jikinsa, ya kashe kansa da wani karamin yaro da kuma raunata mutum biyar, da suka hada da wasu ‘Yansanda. Lokacin da Jami’an Bada Agajin Gaggawa suka iso don dauke wadanda suka jikkata, sai ga wani yaro yazo yana kabbara ya durfafi tare da sace harsasan bindigar  wani Soja sanfurin AK47. Allah ya takaita bai bude wuta ba, ya nufi wani Sojan daban, nan take aka harbe shi har lahira sai dai sakamakon musayar wuta wani farar hula ya rasa ransa” kamar yadda wani ganau ya shaida.

Sai dai ‘Yansanda sunce mutum biyu ne suka rasa ransu 11 kuma suka jikkata a harin na Garejin Munan.

A sanarwar da ASP Murtala R. Ibrahim, Mataimakin Jami’in Yada Labaran Rundunar ‘Yansanda Jihar ta Borno ya sakawa hannu ranar Talata da misalign karfe 1: 35 na Yamma. Wani Dan Kunar Bakin Wake dauke da ababan fashewa a jikinsa ya nufi Rundunar Tsaro ta Mussaman da ke sunturi a yankin Garejin Muna.

Karanta:  Sojojin Najeriya Sun Kutsa Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Maiduguri
Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

490total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.