Myanmar ‘Yan Kabilar Rohingya 37,000 Sun Tsere Cikin Awanni 24’

'Yan kabilar Rohingya mafi akasarinsu Musulmi, suna turereniyar samun abinci, bayanda suka tsere zuwa Bangladesh.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla ‘yan Kabilar Rohingya mafi akasarinsu Musulmi dubu talatin da bakwai ne, (37,000) suka tsere zuwa kasar Bangladesh cikin awanni 24, lamarin da ta bayyana shi a matsayin gudun hijira mafi girma da aka taba gani cikin karamin lokaci tun bayan sabon tashin hankalin da ya barke a kasar Myanmar.

A cewar Majalisar, wannan ta sa yawan ‘yan kabilar Rohingya da suka tsere zuwa daga Myanmar zuwa Bangladesh ya karu zuwa dubu dari da ashirin da biyar (125,000) daga dubu Casa’in (90,000).

Kasashen Duniya na ci gaba da matsin lamba ga gwamnatin Myanmar da Aung San Suu Kyi ke shugabanta, kan ta tashi tsaye, domin kawo karshen kisan gillar da ake yiwa ‘yan kabilar Rohingya a kasar, wadanda mafi akasarinsu Musulmi ne.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya zargi gwamnatin Myanmar da aikata kisan kare dangi, yayinda Ministan harkokin wajen Malaysia tare da Malala Yousafzai suka zargi hukumomin da kauda kansu daga abinda ke faruwa.

Kasashen Pakistan da Iran kuwa, sun bukaci kasashen duniya ne, su dauki mataki kwakkwara kan abinda ke faruwa.

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga zanga a yankin Chechnya dake Rasha, domin yin Allah wadai da yadda ake cin zarafin ‘yan kabilar ta Rohingya.

Asalin Labari:

RFI Hausa

897total visits,1visits today


Karanta:  Odinga Na Son a Ba Sauran ‘Yan Takara Dama a Zaben Kenya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.