Najeriya: ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya ta ASUU ta janye yajin aikin da take yi wanda ta kwashe sama da wata guda tana yi.

Amma kungiyar ta janye yajin aikin ne da kashedin cewa za a biya masu bukatunsu nan da watan Oktoba mai zuwa a cewar jaridar Punch.

Kafofin yadan labaran kasar da dama musamman ma na yanar gizo sun ruwaito shugaban kungiyar ta ASUU Farfesa Biodun Ogunyemi yana kira ga malaman da su koma bakin aiki a yau Talata.

Rahotanni sun an cimma matsaya tsakanin kungiyar ta ASUU da gwamnati ne bayan wasu jerin tattaunawa da aka yi da minisitan kwadago, Chris Ngige a jiya Litinin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar malaman ta shiga yajin aikin ne bayan da gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma ta 2009.

12524total visits,4visits today


Karanta:  Mene ne ya Fusata ASUU ta Soma Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani?

Leave a Reply

Your email address will not be published.