Najeriya ta karbi Jirayen Yaki 5 daga Pakistan

Rundunar Sojin saman Najeriya ta karbi wasu sabbin jiragen yaki guda biyar. Wani katon jirgin dakon kaya ya sauka a tsohon filin sauka da tashin jiragen sama na Soji dake jihar Kaduna.

Jirgin wanda ya sauka da sanyin safiya na dauke da jiragen yakin da gwamnatin Najeriya ta yi odarsu daga kasar Pakistan domin ci gaba da yakin da take da ‘yan kungiyar Boko Haram.

Gwamnatin Najeriya dai a baya ta yi yunkurin siyan jiragen daga kasar Amurka amma hakan bai yuwa ba, bayan da hukumomi a Amurka suka zargi rundunar Sojin Najeriya da lain take hakkin ‘yan Adam a yakin da take yi da kungiyar Boko Haram. Rundunar Sojin Saman ta bayyana cewa za ta yi amfani da jiragen ne wajen fatattakar ‘yayan kungiyar ta Boko Haram dake dajin Sambisa.

Asalin Labari:

Vanguard, Muryar Arewa

1515total visits,2visits today


Karanta:  Marasa Dattako Ke Kalaman Kiyayya – Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.