Tarihin Nasir Ahmad El-Rufai

Nasir Ahmad El-Rufai wani shahararren dan siyasa ne wanda kuma a yanzu yake zababben gwamnan jihar Kaduna a arewacin Najeriya. Shi dai El-Rufai ya rike mukamai da dama a Najeriya wadanda suka hada da babban daracta ta cibiyar kula da sayar da kayan gwamnati da kuma ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja a shekara ta 2003 zuwa 2007.

El-Rufai ya kasance mamba a jam’iyya mai ci a Najeriya wato APC wanda a cikin ta ne aka zabe shi a matsayin gwamnan Kaduna a zaben shekara ta 2015. el-Rufa’i ya fara shiga gwamnati ne a lokacin tsohon shugaban Najeriya wato janar AbdulSalami Abubakar inda ya rike mukamin mai bayar da shawara na musamman a harkar mika mulki.

Kuruciya da Rayuwar Gida
An haifi Nasir El-Rufai a garin Daudawa na karamar hukumar Faskari a cikin jihar Katsina daga kabilar Hausa. Mahaifinsa ya rasu yana da shekara takwas a duniya inda dan uwan mahaifinsa ya dauki nauyin karatun sa tun daga kuruciyarsa inda kuma ya sami halartar makarantar Barewa mafi shahara a arewacin Najeriya inda ya sami babban yabo gami da samun babbar nasarar kammala karatun a matsayin babban dalibi.

Karatu
Nasir El-Rufai ya samu halartar jami’ar Ahmadu Ballo dake Zariya inda ya yi karatun digirin digirgir a fannin duba kasa wanda kuma ya samu lamba ta daya wanda a turance akan kira da First Class.

El-Rufa’i ya samu halarta kwalejin Harvard da kuma Georgetown. Sannan ya samu halartar jami’ar London a shekara ta 2008 gami da kwalejin John F. Kennedy dake Harvard a June 2009.

Siyasa
Mutane da yawa kan kalli Nasir El-Rufai a matsayin wanda baya karbar cin hanci. Hakan ta samar masa samun nasara a fannoni daban daban na siyasa a Najeriya. Ya kasance makusanci ga tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, inda wasu da dama kan kalli Nasir El-Rufai a matsayin mataimaki ga Obasanjo ko kuma ma magaji ta bakin tsohon shubagan hukumar fasa kwauri Mallam Nuhu Ribadu.

Abubuwa da dama da wadansu kan ga cewar suna da wuyar yiwuwa a zamaninsa ya iya samun aiwatar da su. Ciki harda rusau a lokacin sa a matsayin ministan babban birni Abuja. Mutane da dama sun yaba yadda ya kasance yana tsara birnin na Abuja wajen ganin ya tabbatar da ainihin tsarin sa na asali.

A shekara ta 2014, Nasir El-Rufai ya samu lashe zaben share fagen shiga takara a jam’iyyar adawa ta APC inda ya zama dan takarar gwamna na Kaduna. Nasir El-Rufai ya samu lashe zaben gwamna wanda akayi a watan Aprilu na 2015 inda ya kayar da abokin karawar sa wato gwamna mai ci a wannan lokaci Mukhtar Ramalan Yaro na jam’iyyar PDP da kuri’u 1,117,637. Duk da dai an kalubalan ci zaben a kotun sauraron korafe korafen zabe, amma daga bisani kotun ta tabbatar masa da kujerar sa watan Oktoba na 2015.

Gwamnan Jihar Kaduna
Nasir El-Rufai ya kasance gwamna na 22 a jihar ta Kaduna bayan sa samu rantsarwa a ranar 29 ga watan Mayu na 2015. Bayan karbar rantsuwar fara aiki, Nasir El-Rufai ya sanar da cewar da shi da kuma mataimakin sa zasu raba albashin su gami da duk wani alawus gida biyu domin bayar wa a gidauniyar gwamnati kyauta domin samun tallafawa gwamnati ta mike.

A ranar 6 ga watan Agusta na 2015 Nasir El-Rufai ya sanar da cewar jihar Kaduna zata fara asusun bai daya daga ranar 1 ga watan Satumba na 2015 wanda a karshe aka rufe asusun ma’aikatun gwamnati dake bankuna daban daban har guda 470, hakan kuma daga karshe ta samar wa da gwamnatin jiha biliyan ashirin da hudu da dubu dari bakwai (24.7 billion) wanda aka dawo dasu a asusun bai daya dake babban bankin kasa mallakin gwamnatin jihar Kaduna.

Nasir El-Rufa’iya samu rage ma’aikatu da dama a jihar Kaduna domin rage kashe kudi da gwamnati kanyi a ko wanne lokaci wajen tafiyar da mulki daga 19 zuwa 13 wanda hakan ya bashi damar nada kwamishinoni 13 gami da samun sauki na rarar kudi biliyan biyu da dubu dari biyu (1.2 billion) a cikin watannai biyu kacal.

A 2016, Nasir El-Rufai ya kaddamar da ciyarwa a makarantun firamare na fadin jihar Kaduna inda yake ciyar da dalibai akalla miliyan daya da rabi (1.5 million). Sannan ya sako karbar kudin makaranta daga daliban duk wata makarantar firamare ta gwamnatin Kaduna domin saukakawa iyayen yara da basu ilimin farko kyauta.

Shafukan Sada Zumunta
Twitter: Nasir Ahmad El-Rufai
Facebook: Nasir El-Rufai
Instagram: Nasir El-Rufai
Wikipedia: Nasir Ahmad el-Rufai

2972total visits,1visits today


2 Responses to "Tarihin Nasir Ahmad El-Rufai"

  1. Hamisu   July 17, 2018 at 7:55 pm

    Allah yataimaka

    Reply
  2. Muhammadu Buhari Dalibi   October 28, 2018 at 12:19 am

    Mai Rubutu Ya Manta Da Sauran Bayanai Da Baiyiba Kamar Kisan Ta’addanci Wanda Ko A Yakin Duniya Na Biyu Ba’ayi Irinsa Ba Kan Mabiya Shi’a Da Kama Jagoran Islamic Movement In Nigeria Shaikh Zakzaky Da Gwamnan Kaduna Yayi Bisa Goyon Bayan Shugaban Kasa Mr Tyran Buhari Da Rundunar Sojojin Najeriya Suma A Qarkashin Gen Burtai Wannan Ba Adalci Bane Na Rubutu Kaki Bawa Rubutunka Hakkinsa Yadda Ya Dace Nasiru Elrufa’i Dan Ta’addane Kayiwa Masu Karatu Bayani Ta Wadda Zasu Fahimta Ya Kamata Kaji Tsoron Allah.

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.