Nayi Fice a Cikin Shirin Fim Din “Tabbataccen Al’amari” – Bilkisu Shema

Suna na Bilkisu Wada Shema, duk da dai an fi sani na da B-Shema. An haife ni a garin Shema dake cikin Jihar Katsina a Najeriya. Nayi ilimin Firamare nawa a Isa Kaita School of Education sannan kuma na samu ci gaba da karatu na a Community School dake shiyar mu.

Duk da dai cewar ban samu damar ci gaba da karatu ba izuwa babbar kwaleji, amma dai na iya cewa sha’awa ta a fannin karatu ta samu cigaba musamman ma ta yadda na fuskanci cewar yana da matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam. To amma saboda wadan su dalilai hakan bata samu yiwuwa ba.

Muryar Arewa: Bilkisu kin shaida cewar baki samu damar ci gaba da karatu ba izuwa babbar kwaleji. Shin hakan ya faru ne sakamakon shiga masana’antar shirya fina-finai ta Hausa ko kuma wani dalili ne da ya shafi rayuwar ki ta gida?

Shema: Allah Sarki. Ko kadan ba haka bane. Kasan rayuwa kan iya zuwa ma da mutum ta haryar da bai taba zata ba. Sau tari idan hakan ta samu zaka ga akan samu tsaiko a wadansu fannoni na karatu kuma wasu lokutan hakan ka iya janwowa kaga mutum ya katse karatun sa gaba daya ko kuma na wucin gadi.

Bayan faruwar dakatar da karatu na hakika daga baya na samu kaina a cikin ita wannan masana’anta ta fina-finan Hausa wato Kannywood.

Muryar Arewa: To amma a wanne lokaci kika samu kanci a cikin ita masana’antar ta shirya fina-finan Hausa?

Shema: To, duka duka dai ba wani dadewa nayi ba a cikin ta. A halin yanzu ban wuce shekaru biyu ba da shiga. Amma kuma na dan dade da yawa yawan jarumai na ita masana’antar wanda mukan yi mu’amaloli na harkokin da shuka shafi cinikayya dama sauran abubawa masu alfanu.

Muryar Arewa: A cikin ita masana’anta ta fina-finai ta Hausa da wanne jarumi ko kuma jaruma kika fi kusanci?

Shema: Kasan ita mu’amala ta rayuwa idan kana yi da jama’a baka warewa kace ga wanda kafi kusanci dashi. Musamman ma idan ka duba zaka ga cewar ai ita mu’amala ka kan yi ta ne da makusantan ka dama. Saboda haka a kaskiya kowa nawa ne matuwar munzo kusa. Bugu da kari kaga ni ‘yar asalin jihar Katsina ce. Anan na tashi kuma nayi wayo na.

Muryar Arewa: A shiyar ku ta Katsina akwai wata masana’anta ne ta shirya fina-finan Hausa ta daban ko kuma duka daya ce da wacce akan kira Kannywood da ta hada jihohin Arewa gaba daya wacce kusan za’a iya cewa hedikwatar ta tana Kano?

Shema: To kasan dai yawanci kowacce jiha tana da nata kamfanoni wadanda kan shirya fina finai. Kamar kaga za’a iya cewa shiyar nada kamar su FKD da dai sauransu.

Muryar Arewa: Bilkisu kamar yadda kika fara bayar da misali cewar a shiyar Kano akwai irinsu FKD da dai sauran su. Baki ganin zai nuna cewar zai nuna kamar kin fito ne daga bangaren shugaban kamfanin wato Jarumi Ali Nuhu ko kuma dai kawai misali ne kika bayar da sunan kamfanin sa?

Karanta:  Yaushe Ali Nuhu zai daina rawa da waka a fim?

Shema: Na kira sunan FKD ne kawai a matsayin su na kamfanin da ya shahara wajen shirya fina-finai wanda kusan a duk inda ka shiga sanannu ne su. Kuma abu na gaba shine ai Ali Nuhu akan kansa ya kasance mutum na farko wanda ya bani goyon baya da gudunmawar da ta tabbatar dani a matsayin Jaruma a cikin ita wannan masana’anta ta fina-finan Hausa.

Ali Nuhu ya taimaka min sosai a fanni daban daban na shirya fim. Don haka kaga dole na iya bayar da misali dashi kasancewar sa jigo a cikin tafiya a masana’antar Kannywood.

Muryar Arewa: A baya kin ambaci sunan ki da Shema. Shin wannan wani take ne naki na musamman a cikin masana’antar Kannywood ko kuma sunan garin ku ne?

Shema: Shema gari ne a cikin Karamar Hukumar Dutsin Ma wanda kuma ta kasance masarauta. A halin yanzu akwai Kawu na mai suna Abubakar Abdussalam wanda shine ke rike da sarautar Magaji Shema.

Muryar Arewa: Shema gaki Jaruma, kuma ‘Yar Sarauta. Wacce irin nasara kika samu a cikin wannan tafiya? Sannan kuma kikan bayar da gudummawa kasancewar ki Basarakiya ko kuma kawai kina gabatar da shirye shiryen ki na fim ne kawai akan duk wani nau’i da aka dora ki akan sa?

Shema: A gaskiya zan iya cewa na samu ci gaba sosai a wannan tafiya ta Jarumtaka. Musamman ma ta yadda na koyi al’adu da dabi’u wadanda na kanyi amfani dasu domin ci gaban rayuwa ta.

A fannin gudunmawa ai kasan ita Jaruma ta kan doru ne akan duk wani tsari da furodusa ya dora ta, ba wai sai abinda ta gada daga gidan su ba. Don haka ina ganin zan iya duk wani abu da aka bani nayi.

Muryar Arewa: Kina nufin zaki iya yin duk wani abu da aka baki a cikin shirin fim doka misali al’adar ki bata amince ba ko kuma bangaren shiyar ki ta garin Shema a cikin jihar Katsina?

Shema: Kasan saboda addini da ma al’adun mu na kasar Hausa akwai ababan da ma ba za’a dora mu akan su ba, musamman ma mu Jarumai Mata. Don haka ina ganin idan matakin bai saba addini da al’ada ba zan yi iya bakin kokari na domin naga cewar na kamanta shi yadda ya kamata. Dama ai duk bai wuce raye-raye da wake-wake ba wanda kuma duk ba zai gagara ba.

Karanta:  Dalilin da ya sa ake min kallon 'yar wiwi — Hauwa Waraka

Muryar Arewa: Kince raye-raye da wake-wake wadanda kuma ba zasu gagara ba, kina nufin kamar ita kanta rawar da akanyi a cikin shirin fim na Hausa, kina ganin tana cikin al’ada ne ko kuma a’a an kirkire ta ne domin a kara wa shi shirin fim din armashi?

Shema: Ba haka bane. Idan zaka duba fina finan mu na can baya zaka ga akwai rawa da waka da kuma kade-kade. To amma kasan komai ya kan tafi da zamani. A lokutan baya da kuma yanzu akwai banbance-banbance wadanda an canza su da dama. Don haka a yanzu akanyi rawa wacce take ta sha banban da shirin fina finai na baya.

A cikin al’adu ma na Bahaushe akwai rawa kamar irin wacce akan yi a dandali. Amma dai rawa ta cikin shirin fim kan kara masa armashi wanda wadan su masu kallo suna yi ne domin ita kanta rawar.

Muryar Arewa: Shema kinyi bayanin yadda kika shiga masana’antar shirya fina-finai ta Hausa, kina da shekaru nawa a wannan lokaci?

Shema: Na shiga masana’antar Kannywood ina ‘yar sheraka 21.

Muryar Arewa: A yanzu shekarun ki na haihuwa nawa?

Shema: Ina da shekaru ashirin da uku a duniya.

Muryar Arewa: A wacce shekara aka haifi Jaruma Shema?

Shema: An haife ni a ranar 28 ga watan July 1994 (ashirin da takwas ga watan Yuli na alif dari tara da casa’in ta hudu) da misalin karfe biyu da rabi na rana (2:30pm).

Muryar Arewa: Bilkisu Wada Shema gaki da shekarun haihuwa ashirin da uku (23 years) a halin yanzu wanda a garuruwan Hausa kuma musamman ma a Arewacin Nijeriya zaki ga shekaru ne daya kamata ace mace na dakin mijin ta. Shin ko kina da tunanin yin aure a yanzu ko nan gaba?

Shema: Ai duk mace shekaru irin nawa hakika zata so ace tana dakin mijin ta wanda nima naso ace hakan ta kasance. Kuma ko yanzu Allah Ya kawo min zanyi.

A kwanakin baya ai kusan wadanda duk suka sanni da yawa-yawan su sun san cewa na nayi kokarin yin aure. To amma kuma sakamakon wata ‘yar tangarda hakan bata yiwu ba. Kuma a halin yanzu ina addu’a abin da yafi alkairi Allah Ya zaba min.

Muryar Arewa: Wanne shirin fim ne kike ganin shine ya fito dake a masana’antar fina-finan Hausa?

Shema: Akwai Karmatako Studio dake Kano wanda na fito a cikin wani shirin fim din su mai suna “Tabbataccen Al’amari” wanda Zaharadden Musa Karmatako ya shiryawanda a gani na shine fin din da nayi fice a cikinsa kuma mutane suka sanni sosai. Akwai fin din FKD wanda Ali Nuhu ya shirya mai suna “Sallamar So”.

Muryar Arewa: Wanne Jarumi yafi kwanta miki a cikin rai wajen yin shirin fim tare?

Karanta:  'Babu wanda zai sake lashe gasa idan ina Kannywood'

Shema: Bani da wani na daban da zance nafi so. Dun wanda aka hada ni dashi ina iya yin shirin fim dashi musamman ma idan zai taimake ni wajen kara min sani.

Muryar Arewa: Jarumai Mata fa?

Shema: In jin dadi sosai a duk sanda aka hada ni fim da Jamila Nagudu saboda yadda take taimako na sosai. Jamila Jaruma ce hazika wacce ta fini shekaru da kwarewa a cikin harkar fin wadda kan taimaka min sosai wajen koya min abubuwan da ban iya ba.

Muryar Arewa: Yaya kike ganin yadda mutane ke kallon ku a matsayin Jarumai mata?

Shema: A gaskiya na sani cewar mutane da dama kan kalli ‘yan fin a matsayin mutanen banza, musamman ma mu mata, to amma ko kadan ba haka bane. Kamata yayi ace mutane su dinga yi mana adalci kuma su dinga yi mana addu’a koma da ace akwai bata gari a cikin mu.

Muryar Arewa: Jaruma Bilkisu Wada Shema wanne kira zakiyi wa al’umma don su gane cewar wannan kallo da suke muku a matsayin mutanen banza ba haka bane?

Shema: To, ina kira ga mutane a duk lokacin da suka ga munyi wani abu wanda bai dace ba a matsayin su na masu kallon mu suyi kokarin sanar damu domin samun gyarawa. Duk wanda ka gani a cikin wani hali to kayi masa addua. Ance “fal yaqul khairan aw liyasmut”.

Sau tari zaka ga wasu aibata mu kuma su dinne dai masu binmu idan mun fito waje suna sha’awar ganin mu. Don haka su rika mana addu’a.

Muryar Arewa: Shema shin yaya kike kallon shirin fim? Kina kallon sa a matsayin sana’a ko kuma abin sha’awa?

Shema: Gaskiya na fara yin shirin fin ne a matsayin sana’a. Kuma harkar kasuwanci dai dai gwargwado ina yi. Na kan sayi kaya kuma na sayar kamar kayan mata irin takalma da jaka wanda wasu lokutan nakan saka a shafin sadarwa sannan masu sha’awa su biyo har gida su saya.

Muryar Arewa: Jaruma Bilkisu Wada Shema mun gode.

Shema: Ni ma na gode.

9023total visits,24visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.