NDLEA ta kama kilogaram 881.100 na kwayoyi a Sokoto

Hukumar Yakin da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa (NDLEA) tare da sauran hukumomi sun sami nasarar kwace wasu haramtattun kwayoyi da yawansu ya kai kilogaram 881.100, sakamakon wani sumamen hadin gwiwa na musamman da aka gudanar a Jihar Sokoto da kuma wasu yankuna tsakanin bodar Najeriya da Nijar.

Shugaban hukumar, Kanar Muhammad Mustapha Abdallah (Mai Ritaya), ya bayyana hakan a garin Sokoto a ranar Juma’a a wajen rufe taron hadin gwiwa da aka gudanar na tsawon kwanaki biyar akan sanin makamar aiki da atisaye tsakanin Najeriya da Nijar.

Wannan shiri dai kungiyar ECOWAS ce tare da hadin gwiwar Interpol ne suka shirya shi a Sokoto. Abdallah ya kara da cewar, nasarar an same ta ne karkashin wani aiki na hadin gwiwa da aka yi wa take da ‘Operation Ninibo’ a bodar Najeriya da Nijar.

Shugaban hukumar ta NDLEA ya kara da cewa, mutane 6 da ake zargi wadanda suka hada yaro dan shekara 12, an kama su ne yayin sumamen.

Ya bayyana kiddigar abubuwan da aka kama wadanda suka hada da kilogramo 67.10 na Diazepam, 22.60 na Tramadol, 794 na maganin tari wanda ke dauke da Codeine da kuma kilogaram 30 na tabar wiwi.

 

 

 

 

2809total visits,2visits today


Karanta:  Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.