Neymar ka iya sake jinkirta taka leda a Paris St-Germain

Wasan Neymar na farko a Paris St-Germain ka iya sake samun jinkiri saboda har yanzu hukumomin kwallon kafa a Faransa ba su samu takardun amincewa da cinikinsa ba, bayan ya kafa tarihin koma wa PSG daga Barcelona a kan fam miliyan 200.

Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta ba wa takwararta ta Spaniya wa’adin zuwa daren Alhamis domin aika mata takardun amincewa da komwarsa kungiyar PSG a gasar Ligue 1.

Kuma matukar wa’adin ya wuce, Neymar ba zai buga wa PSG wasa a Guingamp ranar Lahadi ba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

594total visits,1visits today


Karanta:  Liverpool Ta Yarda Su Cigaba Da Tattaunawa Da Barcelona Akan Cinikin Coutinho

Leave a Reply

Your email address will not be published.