Niger: Hana Kwararar Bakin Haure Ya Haifar Da Talauci

Tattalin arzikin yankin jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar, na fuskantar koma baya sakamakon hana kwararar bakin hauren da hukumomi suka yi.

Wasu ‘yan kasuwa da ke sayar da kayayyakin da bakin hauren ke amfani da su wajen ketara sahara, sun ce yanzu babu abin da suke fama da shi face yunwa da talauci, saboda ba ma su siyan kayan da suke sayarwa.

‘Yan kasuwar sun ce, yanzu babu abin da suke face zaman kashe wando a rumfuna ko shagunansu.

Su ma masu sana’ar haya da babur da ke jigilar bakin hauren daga tashar mota zuwa masaukinsu, sun ce dakatar da kwararar bakin hauren da hukumomin suka yi, ya jefa su cikin halin ha’ula’i, domin da kyar suke samun abin da za su kai bakinsu.

Wasu masana a Jamhuriyar Nijar din sun ce, duk da kokarin da hukumomin kasar ke yi don magance kwararar bakin masu bi ta hanyar Agadez da zummar shiga kasashen Turai, har yanzu da sauran rina a kaba.

Asalin Labari:

RFI Hausa

1007total visits,1visits today


Karanta:  Tanzania ta Gurfanar da Mutanen da Suka Kashe Mayu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.