Nigeria: An tura jirgin yaki yankin Igbo

Rundunar sojin saman Najeriya ta shiga aikin dakile tashin hankali a kudu maso gabashin Najeriya mai suna 'Operation Python Dance II.

Wata sanarwar da darakatan hulda da jama’a na sojin saman Najeriya, Olatokunbo Adesanya, ya sanya wa hannu, ta ce kayayyakin aikin da sojin saman Najeriya ta tura wa jami’an aikinta na musamman a Fatakwal sun hada da jirgin yaki kirar Alpha Jet.

Sanarwar ta kara da cewar an tura jirgin yankin ne domin a samar wa sojin kasa kariya ta sama domin inganta aikinsu.

An dai fara aikin dakile matsalolin tsaro a yankin kudu maso gabashin Najeriyar ne ranar 15 ga watan Sataumban 2017.

Sojin saman Najeriyar ta ce yawan wurin da aikin zai shafa da kuma bukatar sojin kasan kasar ne ya sa sojin saman suka shiga aikin.

A ranar Litinin tawagar gwamnonin arewacin Najeriya, suka yi wani rangadin shiyyoyin kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar, a wani kokari na shawa kan rikicin.

A baya-bayan nan dai rikicin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a yankin ya yi kamari.

Asalin Labari:

BBC Hausa

591total visits,1visits today


Karanta:  'Yan Kabilar Igbo Mazauna Jihar Naija Sun Yi Watsi Da Yunkurin Kafa Biafra

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.