Nigeria Ce Ta Daya a Yaran Da Basa Zuwa Makaranta — UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kasashen Afrika su ne suka fi fama da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.

Asusun ya ce, Najeriya kuma, ita ce ta fi yaran da ba sa zuwa makarantar a tsakanin kasashem duniya gaba daya.

Wata kididdiga da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta nuna cewa, kashi 46 cikin 100 na yara a Najeriya, ba sa zuwa makarantar gaba da firamare wato sakandire, wanda wannan adadin shi ne kusan rabin yaran kasar.

Wasu yara da BBC ta tattauna da su a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriyar, sun ce dawainiya ce ke wa iyayensu yawa, shi ya sa ba kowanne yaro ne ke zuwa makarantar sakandire ba, yayin da wasu kuma suka alakanta rashin zuwan nasu makaranta da maraici, wato na rashin mahaifi.

Matsalar rashin zuwan wasu yaran makarantun sakadire ba a arewacin Najeriya kadai ta tsaya ba, har ma da kudancin kasar, domin a jihohi kamar Lagos ma, akwai yaran da ba sa zuwa makaranta musamman ta gaba da firamare saboda wasu dalilai.

A shekarar 2016, asusun na UNICEF, ya kaddamar da wani tallafi na samar da dala biliyan biyu da miliyan 800, domin tallafa wa yara a yankunan da ake fama da rikice-rikice a duniya , kuma tallafin ya mayar da hankali ne a kan ilimi.

Batun ilimi na daga cikin abubuwan da suka kasance a zukatan shugabannin kasashen da suka halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72.

Asalin Labari:

BBC Hausa

3003total visits,2visits today


Karanta:  Ambaliya: Trump na neman dala biliyan 8

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.