Nigeria na da muhimmanci a wurina – Bill Gates

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Bill Gates, ya ce Najeriya tana daya daga cikin kasashen da yake sanya ido kansu sosai.

Bill Gates wanda ya bayyana haka a wata hira da BBC, ya ce kasar tana da muhimmanci ne a wurinsa saboda ita ce ta fi kowace kasa yawan al’umma a nahiyar Afirka.

“Wannan ne ya sa gidauniyata ta Bill & Melinda Gates Foundation take ci gaba da aikace-aikacenta a can,” kamar yadda ya ce.

Har ila yau, ya ce akwai babban kalubale a fannin kiwon lafiya a yankin arewacin kasar.

“Akwai matsalar cutar maleriya da kuma batun ‘yan gudun hijira. Muna aiki da wadansu daga cikin gwamnatocin jihohi kamar na Kano da Borno a kokarinmu na ganin mun magance kalubalen kiwon lafiya a yankin,” in ji shi.

Ya ce ayyukan gidauniyarsa suna taimakawa wajen rage mutuwar mata masu juna biyu da kuma kananan yara a fadin kasar.

Sai dai ya ce suna aiki ne tare da gwamnatin kasar da kungiyoyi masu zaman kansa da kuma attajirin nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote – wanda dan kasar ne.

Kamar sauran kasashen Afirka, Najeriya na daya daga cikin kasashen da aka fi yawan samun mace-macen mata wajen haihuwa da kuma na kananan yara.

Asalin Labari:

BBC Hausa

10143total visits,2visits today


Karanta:  Za'a kalli kalaman batanci a matsayin ta'addanci - Osinbajo

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.