Nigeria ta daukaka kara kan wanke Bukola Saraki

Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, ya bayar da umarnin a daukaka kara a kan wanke shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki daga zargin kin bayyana kadarorinsa.

Kuma a ranar Talata ne gwamnatin ta shigar da karar a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, babban birnin kasar.

Mista Malami ya kuma jaddada aniyar gwamnati na kara jajircewa wajen yaki da cin hanci da rashawa, duk kuwa da koma bayan da ake samu a wasu shari’un.

Sanata Abubakar Bukola Saraki dai shi ne shugaban majalisar dattawa kuma mutum na uku mafi girman mukami a Najeriyar.

A ranar Larabar da ta wuce ne dai kotun da’ar ma’aikata ta yi watsi da karar da aka shigar kan mista Saraki a gabanta, bisa dalilan cewa ba a gabatar da kwararan hujjoji ba.

Lamarin da ya sa wasu ke ganin gwamnati ba da gaske ta ke ba wajen yaki da cin hanci da rashawa ba sani ba sabo a kasar.

A shekarar 2015 ne dai aka gurfanar da Sanata Saraki a gaban kotun bisa zargin aikata laifuka 18 da suka jibinci cin hanci da rashawa da kuma bayyana kadarorin da bai mallaka ba a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara da kuma a matsayin sanata.

An yi ta kai ruwa-rana a yayin shar’ar, inda har majalisar dattawa ta yi yunkurin sauya dokar da ta kafa kotun da’ar ma’aikatan, matakin da ya fuskanci suka daga wajen mutanen kasar da dama.

Shugaban majalisar dattawan ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.

Asalin Labari:

BBC Hausa

605total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.