Nigeria za ta fara sayar da takardun lamunin Musulunci

A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da shirin sayar da takardun lamuni na Sukuk wadanda babu kudin ruwa a kansu.

Hukumar da ke kula da basuka ta kasar (DMO) ce za ta kadddar da shirin, wanda aka ware kimanin naira biliyan 100.

A cewar jami’ai, wannan shiri zai taimaka wurin samar da kudaden da za a cike gibin da ake fama da shi a kasafin kudin kasar domin gudanar da wasu manyan ayyuka da suka hada da gina hanyoyi.

Wadanda suka zuba jarinsu a wannan tsari za su ci riba ne ta hanyar kudin da za a rinka biyansu sakamakon amfani da wadannan hanyoyi.

Wannan ne dai karon farko da Najeriya ke kaddamar da wannan tsari na Sukuk.

Shugabar hukamar DMO Misis Patience Oniha ce za ta jagoranci tarurrukan wayar da kan jama’a game da sabon tsarin wanda za a fara a jihohin Kano da Kaduna da Legas da kuma Rivers.

Asalin Labari:

BBC Hausa

2515total visits,1visits today


Karanta:  Nigeria na Cikin Halin Murmurewa - Farfesa Sheka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.