Nnamdi Kanu ya bata

Rahotanni na nuna cewa madugun kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu da iyayensa sun bata.

Hakan na faruwa ne bayan sojoji sun kai samame gidansa a kauyen Afaraukwu da ke jihar Abia da ke kudu maso gabashin kasar ranar Alhamis da maraice.

Wani dan uwan Kanu mai suna Prince Emmanuel Kanu ya shaida wa sashin BBC ta wayar tarho cewa dakarun tsaron hadin gwiwa da suka hada da ‘yan sanda da sojoji sun mamaye gidan mahaifin Kanu inda suka rika yin harbe-harbe inda ya bayyana cewar sun hallaka akalla mutum 22.

Har ila yau, ya yi zargin cewa sojojin sun lalata fadar mahaifinsu wanda basaraken gargajiya ne.

Haka zalika ya ce sojojin sun tafi da wadansu muhimman takardu na dan uwansa da kuma wadansu kayayyaki na gidan.

Prince Emmanuel Kanu ya kara da cewa ba su san inda Nnamdi Kanu yake ba. Amma babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatarwa sashin na BBC wannan zargi.

Sai dai sojojin Najeriya sun ce ba ya gidan lokacin da suka je.

Ana ci gaba da zaman zullumi a yankin Kudu maso gabashin Najeriya, inda aka samu wata hatsaniya tsakanin ‘yan kungiyar neman kafa kasar Biafra ta IPOB da kuma sojin Najeriya da ke gudanar da wani atisaye a yankin. Abin da ya haddasa asarar rayuka da dukiya.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, BBC Hausa

776total visits,1visits today


Karanta:  Wadanne Batutuwa Buhari ya Taras a Nigeria?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.