Osinbajo na shirin yin girgiza a Majalisar Zartarwa

 

Yemi Osinbajo

Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya kammala dukkan shirye-shirye domin yin girgiza a Majalisar zartarwa ta kasa.

Bayanan da suka fito daga wata majiya kumaJaridar The Nation ta ruwaito, ya nuna cewar faruwar na kadan daga cikin tattaunawar da Mukkadashin Shugaban Kasa yayi tsakaninsa da Shugaba Buhari lokacin da ya kai masa ziyara ranar Talata a birnin Landan.

Wannan yunkuri shine ya janyo tsaiko ga rantsar da sabbin Ministocin nan biyu wadanda Majalisar Dattawa ta dade da tantancewa.

A yayin da wannan guguwa ta turnuke tsakanin mambobin wannan Majalisa, akwai alamun cewar za a ajiye wasu daga ciki, yayin da wasu za su samu canjin ma’aikatu a sakamakon girgizar.

Majiyar ta kara da cewar “An gano wasu daga cikin Ministocin na da hannu wajen rura wutar sabani tsakanin Majalisar Dattawa da kuma ta zartaswa”.

 

 

 

Asalin Labari:

The Nation, Muryar Arewa, Abusidiqu

475total visits,1visits today


Karanta:  Kundin Tsarin Mulki: Dan Shekara 35 Zai Iya Tsayawa Shugaban Kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published.