PDP: ‘An tsawwala kudin fom din zabe a Kebbi’

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato PDP ta ce ba za ta iya shiga zabukan majalisun kananan hukumomi da za a yi a jihar Kebbi a yawancin wurare ba saboda karancin kudi.

Idan an jima dai ne za a bude rumfunan zabe domin zaben shugabannin da kansiloli na kananan hukumomin jihar 21.

Jam’iyyar dai ta ce ta tsayar da ‘yan takarar shugabancin ne a kananan hukumomin shida kacal.

Ibrahim Umar Ummai shi ne sakataren watsa labaran ta,

Sakataren yada labaran jam’iyyar ya shaidawa BBC cewa hukumar zaben jiha ta sanya kudin sayan fom na dan takarar shugaban karamar hukuma akan naira 500,000, maimakon naira 100,000 da ake saidawa a lokacin da suke kan mulki.

Haka kuma na Kansila ya kai naira 200,000 maimakon naira 30,000 a baya, ya ce kudin ya yi yawa ba kowa ke da kudi ba musamman a wannan lokaci da kowa ya san babu kudi a hannun jama’a.

Kananan hukumomin sun hada da Gwamdu, da Karfi da Argungun, da Arewa, da Audi. PDP ta zargi hukumar zabe da shirya manakisar da za a hana su fitowa a dama da su a siyasa dan yin mulkin kama karya.

Sai dai kuma an ambato shugaban hukumar zaben jihar Kebbi, Hon Aliyu Mera ya ce tabbas PDP ta nemi a rage kudin, amma hakan ba ta yiwu ba saboda daman an yi doka an amince da kudin, kuma a halin da ake ciki yanzu kaya sun yi tsada musamman yanzu da dala ta tashi.

Masu sharhi kan al’amuran siyasa dai na ganin cewa duk da dadewar da jam’iyyar PDP ta yi ta na mulki a Najeriya, da sauya shekar da gaggan ‘ya’yan ta suka yi zuwa jam’iyyar adawa wato APC, na cikin dalilan da sauran ‘yan jam’iyyar ke fuskantar hakan.

A cewar Malam Abubakar Kyari mai sharhi kan al’amuran siyasa a jami’ar Abuja watakil sun ga babu wanda zai kai labari ne shi ya sa suka labe da tsadar fom.

Karanta:  ‘Yan Sanda Sun Zargi Kwankwasiyya Da Laifi Bisa Rikicin Da Ya Faru Ranar Hawan Daushe
Asalin Labari:

BBC Hausa

684total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.