PDP: Jonathan ya yi murna da nasarar Makarfi a kotun koli

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ya yi murna da nasarar da Sanata Ahmed Makarfi ya yi a kotun kolin kasar.

“Ina taya jam’iyyata ta PDP murna saboda nasarar warware rikicin shugabanci da kotun kolin Najeriya ta yi”, in ji tsohon shugaban a shafinsa na Facebook da na Twitter.

Ya yaba wa alkalan babbar kotun kasar, inda ya ce “Bangaren shari’a na Najeriya ya cancanci girmamawarmu da yabonmu”.

Ya ce wannan hukuncin zai hada kan jam’yyar, kuma babu wanda za a muzgunawa a sabili da wannan lamarin.

Ya taya bangaren Sanata Ahmed Makarfi murna, amma ya yi kira a gare su da kada su ga wannan nasarar a matsayin ta wani bangare na jam’iyyar kawai.

Ya ce kamata ya yi su kwaikwayi tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Janar Yakubu Gowon wanda ya yi shelar ‘Babu masu nasara, babu wadanda a ka ci da yaki’ bayan yakin basasan Najeriya.

A karshe ya yi kira ga wadanda suka bar jam’iyyar saboda matsalolin shugabancin da su koma ‘gidansu na ainihi’ domin gina jam’iyyar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

899total visits,2visits today


Karanta:  Dan Arewa Na Farko Ya Tsaya Takarar Shugabancin Karamar Hukuma A Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.