Qatar ta yi watsi da buƙatun Ƙasashen Larabawa

Ministan Harkokin Wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani ya yi watsi da buƙatun da Ƙasashen Larabawa suka nemi ƙasar ta cika su guda 13, gabanin su dawo da hulda da ita.

A ranar Juma’a ne ƙasashen Saudiyya da Bahrain da Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa suka miƙa wa Qatar buƙata 13 da suke son ta cika, ciki har da rufe gidan talabijin na Al Jazeera.

Har ila yau, sun buƙaci ta rage hulɗa da ƙasashen Iran da Iraqi, sannan ta rufe wani sansanin sojan sama na Turkiyya duk a cikin wa’adin kwana goma.

A farkon watan nan ne kasashen suka yanke hulda da Qatar saboda zargin tana goyon bayan ta’addanci.

Zargin da Qatar ta musanta.

Ministan ya ce abin da ƙasashen suke nema daga Qatar ba mai yiwu ba ne.

Kafar yada labaran Al Jazeera wadda take mallakin kasar Qatar ce ita ma ta mayar da martani ranar Juma’a, inda ta ce hakan wani yunkuri ne na “hana ‘yancin fadin albarkacin baki”.

Asalin Labari:

BBC Hausa

997total visits,1visits today


Karanta:  Kisan Musulmin Rohingya ya yi kama da kisan kiyashin Rwanda – Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.