Qatar: Wani Sanata zai hana Amurka sayar wa Saudiyya makamai

Fitaccen dan siyasar nan na Amurka na jam’iyyar Republican Bob Corker ya ce zai dakatar da sayar wa kasashen yankin Gulf makamai, har sai sun magance takaddamar da ke tsakanin su.

Shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje a majalisar dokokin Amurka, ya yi gargadin cewa ana yi wa yaki da ta’addanci na kungiyar IS kafar ungulu.

Makwanni uku kenan da kasashen Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain da kuma Masar suka yanke duk wata alaka da kasar Qatar, ciki har da rufe sararin samaniya da iyakokinsu.

Kasashen sun zargi Qatar da taimakawa ‘yan ta’adda, da alaka da kasar Iran, zargin da ta musanta.

A ranar Juma’a ne kuma kasashen suka sanya mata sharudda 13 da suke son Qatar ta cika kafin su ci gaba da mu’amala da ita, ciki har da rufe gidan talabijin na Al-Jazeera da yanke mu’amala da kungiyar ‘yan uwa musulmi, da takaita alakar diflomasiyya da Iran.

Sai dai mai magana da yawun gwamnatin Qatar, ya sanar da cewa matakin da wasu kasashen larabawa suka dauka ba komai ba ne face yin katsa landan kan harkokin kasar, kuma iyakokin da suka rufe sun sabawa dokokin kasa da kasa.

Rufe iyakokin dai babbar barazana ce ga attajirar kasar da ta shahara wajen samar da mai da iskar gas, wadda ta kuma dogara da kasashe makofta ta fuskar kayan da ake amfani da su ciki har da kayan abinci.

Idan hakan ta ci gaba da kasancewa, Qatar mai al’uma kusan miliyan uku, za ta dandana kudarta.

A bangare guda kuma kasashen Morocco da Iran sun aike da jiragen dakon kaya makare da kayan abinci da na bukatun yau da kullum zuwa Qatar, duk da cewa Morocco ta ce kayan na agaji ne kawai ba da wata manufa sukai hakan ba.

Karanta:  Qatar ta yi watsi da buƙatun Ƙasashen Larabawa
Asalin Labari:

BBC Hausa

748total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.