Rasha ta Bukaci Amurka Data Dawo Mata da Gidajen Ta

Gidan Rasha a Amurka

Kano, Nigeria – Gwamnatin Rasha ta bukaci Amurka data dawo mata da gidajen ta na Diflomasiyya data kwace sakamakon rikicin kutse kan al’amuran zaben kasar wanda Shugaba Donald Trump ya lashe a watan Nuwamba na shekara ta dubu biyu da shida.

Mai magana da yawun Fadar Klemlin Dmitry Peskov yace ba zai yiwu ba gwamnatin Amurka ta kallafa musu sharudda wajen dawo da gidajen. Sakataren harkokin kasashen waje na Rasha Sergei Lavrov yace wannan fashi da makami ne da tsakar rana.

A watan Disamba ne Amurka ta kori jakadun Rasha guda talatin da biyar sannan ta garkame wadannan gidaje da zargin Rasha da katasalandan da harkokin zaben kasar.

Wakilan gwamnatin Rasha dana Amurka zasu gana a yau Litinin domin samun mafita. Karamin Sakataren harkokin waje na Amurka Thomas Shannon zai karfi bakuncin mataimakin Sakataren harkokin waje na Rasha Sergei Ryabkov a Washington.

Mista Peskov ya shawarci cewar babu wani abu da za’a tattauwa akai. Ya kara da cewa “Muna kallon wannan a matsayin wani lamari da ba zai taba amintuwa ba da gindaya sharudda akan dawo da gidajen, muna la’akari da cewa tilas ne a dawo dasu ba tare da wani sharadi ba.”

Mista Lavrov yace “Wannan ba hanya bace da mutane masu da’a da kuma asali mai kyau sukanyi ba.” Ya ci gaba da cewa a wajen wani taro a Belarus “Ta yaya zaku kwace dukiyar da take da makari na diflomasiyya, mu’amala ta gwamnatayya, takardu ingantattu da, kuma ku dawo da su, ku zama masu kare mutuncin doka ‘abinda yake nawa ne, to nawa ne, kuma abinda yake naku ne, to zamu raba tare da ku’?”

Asalin Labari:

Muryar Arewa da BBC News

972total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.