‘Rashin ilimin mata ne silar yawan mutuwar aure’

Fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, Bilkisu Funtua ta bayyana rashin wayewa da karancin ilimi daga bangaren mata a dalilan da ke jawo mace-macen aure a arewacin Najeriya.

Fittaciyar marubuciyar ta bayyana hakan ne a wata hirar da ta yi da sashen Hausa na BBC.

Marubuciyar wadda aka fi sani da Anti Bilki ta ce ta fara rubutu ne domin samar da mafita ga matsalolin mutuwar aure a arewacin Najeriya.

Duk da cewa babu alkaluma a hukumance, amma an yi kiyasin cewa arewacin Najeriya ne yankin da yafi kowane yanki a Afirka ta yamma yawan mutuwar aure.

Marubuciyar, wacce littafinta na farko shi ne “Allura Cikin Ruwa”, ta nuna takaicinta ga irin halin da ‘ya mace ta sami kanta a kasar Hausa.

“Ita ‘yar Bahaushiya ba ta aje komai ba, sai dai a yi mata aure, ta ci abinci, ta haihu, ta mutu, shi ke nan an kashe rayuwar yarinya Bahausa”, in ji Anti Bilkisu.

A ganinta, samar da ilimin addini da na zamani su ne mafita wajen rage aukuwar mutuwar aure a tsakanin al’ummomin arewacin Najeriya.

Ta kara da cewa idan dai aka ilimintar da ‘ya mace to hakika za a samu raguwar samun sabani a gaidajen aure ta bangaren abin rufin asiri da tarbiyyar yara.

“Idan yarinya na da ilimi ko ba ta yi aiki ba to za ta samu dabarun tsayawa da kafafunta da neman na kai da rage dogaro da miji.

“Za kuma ta zamo uwa ta gari da za ta haifi ‘ya’yan da al’umma za ta yi alfahari da su.”

Ta ce an kai lokacin da ya kamata al’ummar arewacin Najeriya su tashi tsaye don ganin an rage samun wannan matsalar, kamar yadda ba a cika samu ba a Kudancin kasar.

Jihar Kano a Najeriya na cikin jihohin da matsalar mutuwar aure tafi yawa a arewacin Najeriya.

Karanta:  'Muna cikin ƙunci da baƙin ciki a yankin Igbo'

Watakila wannan ne dalilin da yasa jihar ta samar da wani shiri na daura wa zawarawa aure.

A karkashin shirin, gwamnatin jihar na hada daruruwan zawarawa a wuri guda a yi bikin daurin auren nasu.

Bayan an daura auren, gwamnatin jihar kan ba ma’auratan shawarwari na musamman da tallafin domin hana aikuwar irin wannan matsalar a gaba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

2896total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.