Rasuwar Dan Masanin Kano

Wata sanarwa daga iyalan marigayi Alhaji Dr. Yusuf Maitama Sule ta tabbatar da rasuwar sa a daren jiya Lahadi a garin Alkahira dake kasar Misra bayan wata ‘yar gajeriyar rashin lafiya. Majiyar ta shaidawa Muryar Arewa cewar ya rasu ne a wani asibiti dake kasar Misra a ranar Lahadi 2 ga watan July 2017.

Marigayi Dr. Maitama Sule shaharraren dan siyasa ne kuma masanin tarihi wanda yayi fice ta fannoni daban daban musamman ma wajen bangaren diplomasiyya inda ya rike mukamin jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1979.

Wata majiya daga garin na Kano ta shaida cewa za’ayi jana’izar sa da misalin karfe biyu na ranar Talata a fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

621total visits,1visits today


Karanta:  Igbo Mazauna Adamawa Na Goyon Bayan Najeriya a Matsayin Kasa Daya

3 Responses to "Rasuwar Dan Masanin Kano"

 1. muhammad sani   July 9, 2017 at 11:20 am

  allah yjikansa

  Reply
 2. muhammad sanade   July 10, 2017 at 8:56 am

  Allah yai masagafara,ameen

  Reply
 3. muhammad sanade   July 10, 2017 at 8:57 am

  Allah yai masagafara,ameen

  Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.