Rikici ya Tilastawa ‘Yan Rohingya 90,000 Tserewa Zuwa Bangladesh

Wasu 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikici yayinda suka tafiya cikin tabo a kan iyakar Myanmar da Bangladesh, ranar 1 ga Satumban 2017.

Hukumomin agaji sun yi gargadin cewa Sansanonin ‘yan gudun hijira a kasar Bangladesh zai iya fuskantar tarin matsaloli saboda yawan jama’ar da ke cikinsa, tun bayan karuwar dubban Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da ke ci gaba da tururuwa cikinsa don gujewa rikicin Myanmar.

Majalisar Dinkin Duniya tace ‘yan kabilar ta Rohingya akalla dubu 90,000 ne yanzu haka suke samun mafaka a kasar Bangladesh tun bayan barkewar rikicin da aka samu a yankin su ranar 25 ga watan Agusta.

Matakin ya biyo bayan hare haren da sojojin Myanmar suka kaddamar Jihar Rakhine wanda yanzu haka yayi sanadiyar kashe daruruwan mutane.

Mafi akasarin ‘yan gudun hijirar wadanda mata da kananan yara suka fi yawa, kan yi korafin yunwa sakamakon daukar tsawon kwanaki basu ci abinci ba.

Wani daga cikin ‘yan gudun hijirar daya tsira da rayuwarsa ya shaidawa manema labarai cewa, sai da ya biya dala dari da hamsin kan kowanne daya daga cikin iyalinsa, kafin a dauko su a kwale-kwale a tsallako da su Bangaladesh.

Asalin Labari:

RFI Hausa

468total visits,1visits today


Karanta:  An Kama Wadanda Suka Yi Wa Wata Mata Fyade a Mota

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.