Roger Federer ya lashe kofin Wimbledon na 2017

Roger Federer

Dan wasan tennis Roger Federer ya lashe kofin Wimbledon na bana bayan ya doke Marin Cilic.

Ya doke Cilic ne da ci 6-3 6-1 6-4, wanda rabon da ya lashe kofin tun a shekarar 2012.

Federer mai shekara 35 ya kafa tarihi na zama dan wasan tennis na farko a duniya da ya lashe kofin sau takwas.

Har ila yau, Federer wanda dan kasar Switzerland ne kuma shi ne dan wasa ma fi shekaru da ya lashe gasar Wimbledon tun bayan da aka sauya mata suna zuwa Open.

Asalin Labari:

BBC Hausa

399total visits,2visits today


Karanta:  Sadio Mane na daf da dawowa atisaye

Leave a Reply

Your email address will not be published.