Ronaldo Ya Kammala Hutun Dole

Mai horar da kungiyar Zinaden Zidane ya bayyana fatan Ronaldon ba zai sake fuskantar irin wannan hukunci mai tsauri ba.

Cristiano Ronaldo zai haska a wasan da Real Madrid zata fafata da Real Betis a gobe Laraba, bayan kammala wa’adin da aka deba masa na haramcin wasanni 5 a gasar La-liga, wanda hukunci ne bisa samunsa da laifin hankade alkalin wasa a fafatawar da suka yi da Barcelona, a gasar Super Cup, wanda Madrid din ta lallasa ta da kwallaye 3-1.

Mai horar da kungiyar Zinaden Zidane ya bayyana fatan Ronaldon ba zai sake fuskantar irin wannan hukunci mai tsauri ba.

Mai yiwuwa hutun dolen da Ronaldon ya samu, ya yiwa kingiyar ta Real Madrid amfani, idan akai la’akari da cewa zai dawo ne da karfinsa.

Idan ba’a manta ba, a gasar Zakarun nahiyar turai da ta gabata, Ronaldo ya samu jefa kwallaye 10 a ragar abokan hamayyarsu, a wasannin da ya buga daga matakin kusa da kusa dana karshe zuwa kammala gasar, bayan warkewarsa daga raunin da ya samu.

Asalin Labari:

RFI Hausa

2552total visits,6visits today


Karanta:  World Cup: Argentina Na Ci Gaba Da Fafutika

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.