Ronaldo ya koma atisaye a Real Madrid

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Portugal, Cristiano Ronaldo ya koma atisaye tare da ‘yan wasan Real Madrid domin tunkarar wasannin bana.

Ronaldo wanda ya lashe kofin Zakarun Turai da na La Liga a Madrid a kakar da ta kare, ya kammala hutun da kungiyar ta amince ya yi, bayan da ya buga wa Portugal Confederations Cup.

Dan kwallon bai buga wa Madrid wasan da ta yi rashin nasara a hannun Manchester United a bugun fenariti a gasar International Champions Cup ba.

Haka kuma bai yi fafatawar da Manchester City ta ci Real 4-1 ba, da wasan da Barcelona ta doke ta ba duk a gasar ta International Champions Cup.

Real Madrid wadda ta lashe kofin Zakarun Turai za ta fafata da Manchester United a wadda ta ci Europa a UEFA Super Cup a ranar Talata a Skopje, Macedonia.

Asalin Labari:

BBC Hausa

671total visits,3visits today


Karanta:  Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona

Leave a Reply

Your email address will not be published.